BOKO HARAM: Kungiyar Red Cross ta roki Najeriya ta sa baki a sako ma’aikatan ta

0

Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), ta yi kururuwar neman agaji daga gwamnatin tarayyar Najeriya, dangane da barazanar da Boko Haram suka yi cewa za su kara kashe ma’aikaciyar kungiyar daya.

Shugaban Kungiyar mai kula da ayyuka a yankin Tafkin Chadi, Mamadou Sow ne ya yi wannan rokon, bayan da Boko Haram suka fitar da sanarwar cewa cikin awa 24 za su kara bindige ma’aikaciyar Red Cross daga cikin wadanda suka kama.

Sow ya roki Gwamnatin Tarayya da kuma daidaikun jama’a su sa baki a sako ma’aikatan sa biyu da yanzu ke a hannun Boko Haram.

Sow ya bayyana sunayen wadanda Boko Haram din suka kama cewa akwai Hauwa Mohammed da Alice Loksha.
Ya kara da cewa akwai bukatar a yi gaggawar shiga tsakani, domin awa 24 Boko Haram suka bada wa’adi cewa za su kara kashe wata ma’aikaciyar Red Cross.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES ta bayar da rahoton kashe wata ma’aikaciyar Red Cross mai suna Saifura Khorsa da Boko Haram suka yi, bayan sun kama su, a cikin watan Satumba.

Boko Haram sun kashe Saifura cikin Satumba, watanni shida bayan sun kama ta tare da abokan aikin ta, Hauwa da Alice a cikin watan Maris.

Sow ya kara da cewa wadannan mata da aka sace su ne daidaikun da suka rage su na gudanar da ayyukan jinkai da agaji a sansanin gudun hijira da ke Rann, bayan da alahirin ma’aikatan lafiya na agaji suka tsere da boda tsoron rasa rayukan su.

Ya ce wadanda ke tsare da Leah Sharibu ne ke tsare da Hauwa da Alice, kuma su ne suka kashe Saifura a cikin watan Satumba.

Share.

game da Author