Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Abba Ibrahim ya karyata cewa da aka yi wai ya ce ko da magudi Buhari ba zai ci zaben 2019.
idan ba a manta ba yayin da yake jawabi a taron kaddamar da wani littafi a Abuja, Bukar ya ce, “Siyasa Arewa maso Gabas a ko da yaushe ta na shan bamban da ta Arewa maso Yamma, domin ain kowa ya san cewa a lokacin APC ne muka samu hadin kai a yankin a karo na farko. Saboda jama’a na tunanin cewa idan ya ci zabe abubuwa za su canja.
“Amma yanzu da muka kusanci zaben 2019, dole na yi kakkausan gargadin cewa abubuwa fa a yanzu ba kamar yadda suke a 2015 din da aka sani suke a yanzu ba.
Domin Buhari dai guguwa ce kawai ta fizge jama’a har suka zabe shi a 2015.
Sai dai kuma a wani bidiyo da aka fitar yana ganawa da manema labarai, Bukar ya ce ” Maigida na Muhammadu Buhari, na mara masa baya a da kuma har yanzu ma ina tare da shi. Tare za mu yi nasara a zaben 2019. Zai ci zaben sa kuma sai ya cike sauran shekaru hududn da ya rage masa.
” Idan dai ina raye Buhari ba zai fadi zabe a yankin Arewa maso Gabas ba, wato jihohin Bauchi, Taraba, Adamawa, Yobe da Barno. Idan Allah ya yarda Buhari ne zai lashe zaben 2019 kuma yayi ta zarce.
” Ni Abba Ibrahim dan Jam’iyyar APC ne, kuma ina jam’iyyar har-illa-masha-Allahu.
Ya bayyana cewa wadanda suka rubuta wai ya ce ko da magudi ba Buhari ba zai ci zabe ba karya suke. Ba su fadi ainihin abinda ya ce ba.
” Abinda na fadi ba haka bane. Cewa nayi ina so muma mutanen yankin Arewa maso Gabas mu tabbata mun nuna wa Buhari irin kwaunar da mutanen Arewa maso Yamma suke nuna masa.