Ma’aikatar Ilmi ta Tarayya ta musanta zargin cewa gwamnatin tarayya ta fara shirin tsawwala kudin shiga jami’o’in Najeriya zuwa naira 340,000.
PREMIUM TIMES ta rubuta labarin cewa kungiyar Malaman Jami’o’i ta yi zargin gwamnatin na kokarin yin karin kudaden shiga jami’o’i.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi, Sonny Echono ya bayyana cewa ba gaskiya ba ne, babu wani zance kokarin yin karin kudin shiga jami’a.
Ya yi wannan bayanai a wurin wani taro, a Abuja, a lokacin da ya ke jawabi.
Daga nan sai ya roki ‘yan Njaeriya da su kwantar da hankaulan su, domin maganar dai ba gaskiya ba ce. Inji shi.
Ya ce abin da ke akwai dai shi ne gwamnatin tarayya ta jaddada kudirin ta na samar da ingantaccen ilmi a Najeriya.
“Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci ma’aikatar ilmi da ma’aikatar harkokin kudade, su hadu su shirya taron sanin yadda za su fitar da hanyoyin da za a rika samun kudaden tafiyar da harkokin ilmi a kasar nan.”
Daga nan sai Echono ya ce kuma ana ta tuntubar masu fada-a-ji a harkokin ilmi, ciki har da kungiyar malaman jami’o’i domin samun hanyoyin tara kudaden.
Ya kara da cewa ana shawarar kafa wa fannin ilmi bankin sa na musamman.