Dan Majalisar Tarayya, Alhassan Doguwa, ya yi watsi da jita-jitar da ake yadawa cewa akwai yiwuwar a tsige Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara.
Doguwa ya bayyana haka a cikin wani sakon ‘tes’ da ya turo wa PREMIUM TIMES, ya na mai kara cewa kakakin majalisa na da ‘yancin shiga duk jam’iyyar da ya ga dama.
“Jita-jitar da ake ta watsawa cewa za a tsige Kakakin Majalisa saboda ya canja jam’iyya, ba fa gaskiya ba ne.
“Shi ma fa ya na da ‘yancin shiga duk jam’iyyar da hankalin ya fi kwanciya a cikin ta, kamar kowane dan Najeriya.
“ Tabbas dukkan mu ‘yan APC ba mu ji dadin ficewar sa ba da kuma rudanin da ke faruwa. Amma kuma tilas mu sani cewa Dogara bai fa aikata wani laifin da ya karya dokar kasa ba.”
Ya ci gaba da cewa sannan kuma don dan majalisa ko kakakin majalisa ya fice daga jam’iyyar, to bai karya wani tsari ko dokar majalisa ba ko kundin tsarin mulkin Najeriya ba.
“Mu dai a matsayinmu na wadanda suka san yadda majalisa ta ke, ba mu yin wani tunani na tsige kakakin majalisa, domin bai aikata laifin da za a tsige shi ba.”
Ya ce kowane mamba kuma kowane dan jam’iyya zai iya rike ofishin Kakakin Majalisar Tarayya da na Mataimakin sa.