Dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar na yin ganawar sirri da tsohon gwamnan jihar Anambra Peter Obi a gidan sa dake Abuja.
Ko da yake ba a bayyana ainihin dalilin wannan ganawa ba, alkaluma duk sun nuna cewa da walakin shine zai zama mataimakin Atiku a takara.
A cikin wadanda ake jerowa wai sune zasu iya zama mataimakin dan takarar PDP din sun hada da shi Peter Obi, sannan akwai tsohuwar ministan Kudi Ngozi Okonjo-Iweala.
Atiku ya doke yan takara 11 a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka gudanar a zaben da ya gabata.
Zai fafata da dan takarar jam’iyyar APC, wato shugaba mai ci a yanzu, Muhammadu Buhari.
Discussion about this post