A yau Litini ne sojojin Najeriya da ‘Yan shi’a suka kaure da gumurzu inda aka yi ta batakashi a tsakanin ‘Yan shian da sojoji.
Wani wanda abin ya faru a idonsa ya bayyana cewa sojojin sun afka wa ‘Yan shia ne bayan sun kafe cewa sai sun bi ta shingen sojoji da ke babban titin Maraba.
” Sojojin sun tararraye su domin su hakura su koma amma kafin ka ankara sai suka fara yi wa sojojin ruwan duwatsu da sanduna inda a garin neman kare kansu sai rikici ya barke aka yi ta batakashi a tsakanin juna.” Haka ya fadi.
” Haka ya sa sojoji suka bude wuta inda har mutane 16 su ka rasu nan take. Sannan wasu da yawa suka samu rauni.
Wani ko da shima hakan ya faru a gaban sa cewa yayi sojojin ne suka fara yi wa masu tattakin ruwan wuta bayan sun kafe sai sun bi ta shingen sojojin.
Bayan haka motoci da ke kan hanyar suka tsorata suka rika buge masu zanga-zangan har wasu suka kararraye.
Daga nan ne fa sojoji suka rufe hanya kwata-kwata domin samar wa mutanen da basu ji ba basu sha ba lafiya. Da yawa dai daga cikin wadanda suke zama a garuruwan Karu, Nyanya, maraba duk sun dawo cikin gari ne domin su kwana.
Idan ba a manta ba a ranar Asabar ne rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewa ‘yan Shi’ah uku ne suka rasu a gumurzu da aka yi tsakanin mabiyan shi’ah da sojojin Najeriya a garin Zuba.
Daruruwan mabiya ne suka tare hanyar Zuba zuwa Abuja a wannan rana inda suka hana motoci wucewa.
A daidai suna haka ne sai kuma ga tawagar wasu motocin sojoji dauke da makamai za su kai Kaduna.
Kwamandan Barikin Soji dake Abuja, James Nyam, ya ce da sojojin suka iso wannan wuri sannan suka nemi ‘Yan Shi’an su basu hanya su wuce sai suka ki.
” A daidai wannan tawagar sojoji na kokarin ganin wadannan masu tattaki sun kauce da ga hanyar ne, sai suka fara harbe harbe da duwatsu da makamai.
” Suka rorrotsa wa mutane da sojoji motoci sannan suka nemi kai wa gare su. Daga nan ne fa sojojin suka nemi karin ma’aikata domin kare kan su da makaman fa suke tafe da.
Daga karshe aka fatattaki masu tattakin aka baza su sannan matafiya da su kan su sojojin suka kama gaban su.
Discussion about this post