APC ta zama gawa a Taraba -Mama Taraba

0

Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Aisha Alhassan, wanda a yanzu ita ce ‘yar takarar gwamnan jihar Taraba a karkashin jam’iyyar UDP, ta bayyana cewa ta na da yakinin samun nasara a zaben 2019.

Jummai wadda tsohuwar Sanata ce, ta bayyana haka jiya Laraba a Abuja, a lokacin da ta kai ziyara ofishin UDP na kasa a Abuja, tare da shugabannin jam’iyyar na jihar Taraba.

Sun kai ziyara ne ga shugaban jam’iyyar, Godson Okoye, inda ta bayyana cewa a yanzu APC ta mutu a jihar Taraba.

Ta ce ba jam’iyya ce ke sa a ci zabe ba, sai tsarin da jam’iyya ta yi nagari da kuma dimbin magoya bayan ta.

Jummai, wadda aka fi sani da Mama Taraba da Minista Adebayo Shittu an ki tantance su ne a takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC.

Ta ce a yanzu haka ta fi magoya baya da ta shiga UDP, fiye da can baya. Sannan kuma ta kara da cewa APC ta yi mata rashin adalci, amma rashin adalcin ya zame mata alheri shigar ta UDP.

Ta ce a yanzu al’ummar jihar Taraba sai rububin shiga jam’iyyar UDP kawai suke yi, tare da neman katin shaidar dan jam’iyya.

Tuni inji ta su buga katin shaidar dan jam’iyyar har 120,000, kuma ya kare a cikin sati biyu, har ana neman kari domin bai wadata ba.

Share.

game da Author