Hukumar kula da ingancin kayayyaki a Najeriya (SON) ta bayyana cewa za ta sa ido don ganin ta hana shigowa da wasu magungunan da kasar Chana ke sarrafawa da naman mutattun mutane Najeriya.
Jam’in hukumar Bola Fashina ya fadi haka inda ya bayyana cewa hukumar su ta sami labarin haka ne a wata wasika da aka aiko mata, hukumar Kwastam da NAFDAC.
Fahina ya ce wasikar ta bayyana yadda kasar Sin ke sarrafa wasu kwayoyin magunguna da naman jikin mutanen da suka mutu a dalilin kamuwa da cututtuka kamar su kanjamau, Hepatits sa sauran su.
Wasikar ta bayyana cewa amfani da wadannan kwayoyi na cutar da lafiyar mutum ganin cewa mutum zai iya kamuwa da wadannan cututtuka da ya yi ajalin wadannan mutane.
Fashina yace za su kara zage damtse don ganin sun hana wadannan magunguna shigowa kasar duk da cewa wannan aiki na hukumomin NAFDAC ne da Kwastam.
Bayanai sun nuna cewa arewa maso gabashin kasar Sin ne ke sarrafa wadannan kwayoyi.
Discussion about this post