Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da sassauta dokar hana zirga-zirga a fadin jihar.
A sanarwan da Kakakin gwamnan jihar Samuel Aruwan ya fitar Yau Lahadi, ya ce daga gobe Litini 29 ga watan Oktoba, za a rika walwala daga karfa 6 na safe ne zuwa karfe 5 na yamma.
Sannan kuma gwamnati ta yi kira ga hukumomin jiragen Sama da na Kasa da su dawo da ayyukan su na jigilar fasinjoji zuwa garin Kaduna.
Takardar ta ce bankuna da ma’aikatu za su bude daga gobe.
Discussion about this post