Lauyan tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose, ya bayyana cewa an saki wanda ya ke karewa din a jiya Litinin, dayan ya shafe makonni biyu a tsare.
An sake shi ne bayan ya cika sharuddan belin da kotu ta gindaya masa, wadanda aka yi kwanaki biyu kafin a samu ya cika.
Lauyan sa Mike Ozekhome, ya bayyana wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa an saki Fayose jiya Litinin da yamma, kuma har tsawon wani lokaci ma su na tare bayan sakin sa da aka yi.
Ya ci gaba da cewa Fayose na nan garau, kuma zai ci gaba da fafutikar ganin an kawar da wannan gwamnatin da makafin da ba su san hanyar da suka dosa ba ke mata jagora.
Shi ma kakakin yada labaran sa, Lere Olayinka, ya rubuta a shafin sa na twitter cewa an saki Fayose jiya Litinin da yamma. Ya aika da sakon ta shafin twitter na, jimkadan bayan da Fayose ya fice daga kotun da cika umarnin belin na sa a Lagos.