Gwamnatin jihar Kaduna ta saka dokar hana fita da walwala na awoyi 24 a garin Kasuwar Magani dake karamar hukumar Kajuru.
Kakakin gwamnatin jihar Kaduna, Samuel Aruwan ne ya sanar da haka a takarda da ya fitar yau daga fadar gwamnatin jihar.
Gwamnati tace ta yi haka ne domin ta dakile rashin zaman lafiya da ke neman ya barke a garin.
Discussion about this post