Jami’ar Cibiyar ‘Global Partnership for Education (GPE)’ da ‘Teacher Professional Development (TPD)’ Halima Jumare ta bayyana cewa a cikin watanni biyu da suka gabata gwamnatin jihar Kaduna ta horas da malamai da ma’aikatan makarantun firamare 5,834.
Halima ta sanar da haka ne a hira da ta yi da Kamfani Dillancin Labaran Najeriya a Kaduna.
” Mun horas da malaman ne kan yadda za su iya karkato da hankulan dalibai ta hanyoyin dabam-dabam kamar ta wakoki da suran su.
Halima ta ce a yanzu haka wasu malamai 4,742 na samun irin wannan horon bayan 5,834 din da aka fara horaswa.
Discussion about this post