Rundunar Sojin Najeriya ta sanar cewa ta gano ramin da aka fara bizine janar Alkali Mohammed da ya gamu da ajalin sa a hanyar sa ta zuwa garin Bauchi daga Abuja.
A bayannan da sojojin suka bayar sun ce wannan kabari da suka gano shine ramin farko da aka bizine marigayi janar Alkali bayan an kashe shi kafinnan kuma a ka canja masa wuri.
Shi dai marigayi Janar Alkali ya bace ne tun daga ranar 3 ga watan Satumba a hanyar sa ta zuwa garin Bauchi daga Abuja, inda ake kyautata zaton wadanda suka yi garkuwa dashi suka kashe shi.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda aka tsinci motar sa a cikin wani rami mai kama da kududdufi a garin Dura Du dake jihar Filato.
Tun bayan wannan lokaci da aka tsici motar janar Alkali a wannan kududdufi, rundunar soji ta zurfafa bincike in da aka samu wasu daga cikin kayan sawarsa da takalmin sa kafa daya sannan kuma a kayi kamen mutane 30.
Janar B. A. Akinruluyo, na barikin soji da ke Rukuba ya bayyana yadda rundunar ta gai ga wannan rami da aka fara bizine janar Alkali.
” Ina so mutane su sani cewa mutane dabam-dabam har hudu da basu san juna duk sun kaimu wannan rami inda suka ce a nan ne aka fara bizine janar Alkali.
Bayan haka mun saka karnukan mu dake da kwarewa wajen sunsuna abu ko wuri, sun sunsuna wannan rami sun tabbbatar an bizine marigayin a nan kafin aka sake hake shi aka canja wuri.
Bayannan Janar B. A. Akinruluyo ya yi kira ga mutanen garin da su ci gaba da ba rundunar sojin hadin kai sannan duk wanda yake da wani masaniya kan inda aka bizine janar Alkali ya taimakawa sojin.
Ya kuma kara da cewa rundunar soji za ta tabbata ba a tauye wa mutane hakkin sa a matsayin ‘yan kasa ba a wannan aiki da suka sa a gaba.