Wasu likitoci a wani asibitin yara dake Philadelphia da likitocin jami’ar Pennsylvania, kasar Amurka sun gano cewa maganin BE3 na kawar da cutar dake kama yara tun suna cikin uwayen su da ake kira ‘Congenital Disease’.
Likitocin sun bayyana cewa cutar kan nakasa wasu bangarorin jikin jariri ne sannan a wasu lokuttan sa’an cutar kan bayyana bayan yaro ya fara girma.
Jarirai kan kamu da wannan cutar idan mahaifan su mata na shan taba sigari ko kuma shan giya, rashin cin abincin dake gina jiki, yawan shakar maganin feshi, canjin yanayi da sauran su a lokacin da suke dauke da ciki. Sannan bayanai sun nuna cewa ‘ya’ya kan gaji wannan cuta daga jikin iyayen su.
Alamomin wannan cutar sun hada da kamuwa da cutar dajin dake kama hanta, rashin kaifin kwakwalwa, kumburin kafafuwa da zuciya da dai sauran su.
Jagorar wannan binciken Kiran Musunuru ta bayyana cewa sun gano wannan maganin ne yayin da suke gwada ingancin maganin a jikin wasu beraye dake da ciki inda suka sha ruwan wannan magani na tsawon kawani uku.
” Da muka gwada ‘ya’yan berayen da aka haifa sai muka ga cewa wannan maganin BE3 ya kare su daga wannan cuta.
Musunuru ta ce basu da tabbacin ingancin wannan maganin a jikin mutum amma ta yi kira ga mata masu ciki da su guji yin abubuwan da ka iya cutar da kiwon lafiyar ‘ya’yan su musamman a lokacin da suke da ciki.
A karshe amfani da maganin Folic Acid, gwajin cutar a asibiti da cin abincin dake inganta garkuwar jiki na daga cikin hanyoyin da mace mai ciki za ta iya kiyayewa domin kare ‘ya’yan ta daga kamuwa da wannan cutar.