Shugaban kungiyar ma’aikatan kamfanin jiragen saman Najeriya ‘Nigerian Airways” da suka yi ritaya Godwin Jibodu ya bayyana cewa gwamnati ta fara biyan ma’aikatan kamfanin da suka yi ritaya kashi 50 bisa 100 daga cikin kudaden fanshon su.
Jibodu ya sanar da haka ne ranar Litini wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jihar Legas.
Sannan ya kara da cewa bashin kudaden da wadannan ma’aikata ke bin gwamnati ya kai Naira biliyan 22.6.
” Wannan abun farin ciki ne a gare mu ganin cewa gwamnati ta cika alkawarin da ta dauka.
Ya ce yanzu haka gwamnati na tattance ma’aikatan kamfanin a jihohin Legas, Kano da Enugu.