Gwamnatin Kaduna ta sanar da dawowa da dokar hana zirga-zirga a garin Kaduna da kewaye, da garin Kateri, karamar hukumar Kachia, Chukun da Kasuwan Magani.
Idan ba a manta ba an sassauta dokar a ranar Alhamis, daga karfe 6 zuwa 5 na yamma.
Gwamnati ta ce ta yi haka ne domin a samu natsuwa a jihar sannan ayi juyayin kashe sarkin Adara da masu garkuwa suka yi garkuwa da a makon da ya gabata.
A sanarwar gwamnati ta ce kowa ya koma gida daga karfe 11 na safe har sai illa ma-sha-Allahu.
Daga nan sai gwamnati ta yi kira ga mutanen gari da su zauna da juna lafiya, sannan a daina kokarin ta da zaune tsaye.