An dakatar da shugaban Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa, Yusuf Usman, sai illa-masha’Allahu

0

A yau ne shugaban hukumar gudarwa na hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa Ifenne Enyanatu, ta bayyana cewa kwamitin gudarwa nahukumar ta dakatar da shugaban hukumar Yusuf Usman sai Illa-masha’Allahu.

Enyanatu ta bayyana haka ne cewa kwamitin ta dauki wannan mataki ne bayan saurari korafe-korafe da dama game da yadda Yusuf yake shugabantar ma’aikatar da suka hada da sama da fadi da kudade, taurin kai da nuna iko a aikin sa.

” Bayan mun tantance wadannan korafe-korafe sai muka aika wa ministan Lafiya, Isaac Adewole. Da ya duba sai ya amince mana da mu dakatar da shi domin a gudanar da bincike akai.”

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya ne ministan kiwon lafiya Adewole ya dakatar da Yusuf Usman ba sa ga zargin babakere da yayi da kudaden hukumar NHIS.

A wancan lokaci Adewole ya bayyana wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf shine don korafe korafen da ake tayi akansa na yin sama da fadi da kudaden ma’aikatar da kuma zargi da akeyi masa na aikata wasu laifuka da ya saba dokar hukumar.

Minista Isaac Adewole ya ce ya dakatar da Usman Yusuf na tsawon watanni uku ne saboda a sami damar gudanar da bincike kan zargin da akeyi a masa.

Ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su tabbata sun saka ido akan takardun ma’aikata har zuwa a kammala bincike.

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya ce wasu daga cikin dalilan da ya sa ya dakatar da shugaban hukumar inshorar lafiya lafiya ta kasa NHIS Usman Yusuf shine don korafe-korafen da ake tayi akansa na sama da fadi da yayi da wasu kudaden ma’aikatan da kuma zargi da akeyi masa na aikata wasu laifuka da ya saba dokar ma’aikatar.

Minista Isaac Adewole ya ce ya dakatar da Usman Yusuf na tsawon watanni uku ne saboda a sami damar gudanar da bincike akan zargin da akeyi a kansa.

Ya yi kira ga ma’aikatan hukumar da su tabbata sun saka ido akan takardun ma’aikatan har zuwa a kammala bincike.

Share.

game da Author