Kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa za ta tallafa wa mutanen da ambaliyar ruwa a Najeriya ya shafa ta hanyar samar musu da magunguna da sauran ababen tallafi.
WHO ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa mutane 826,000 ne ambaliyar ruwa ya shafa a dalilin cikowar kogin Neja da Benuwai a watan Agusta inda aka rasa gidajen 176,800, gonaki 150,000 , tituna da gadaje 321 a jihohi 12 a Najeriya.
Binciken ya kuma nuna cewa bana ambaliyar ta ci rayukan mutane 200.
Shugaban WHO Wondimagegnehu Alemu ya bayyana cewa a dalilin haka ne suka amince su tallafa wa gwamnatin Najeriya ta hanyar ganin ba asake samun irin haka ba.
Alemu yace samar da magunguna ya zama dole musamman yadda mutanen da ambaliyar ta shafa kan yi fama da cututtukan amai da gudawa, ciwon ciki da sauran su.
A karshe ya kuma ce kungiyoyin ‘Red Cross da Red Cescent’ sun bada gudunmawar dala miliyan 5.5 domin tallafawa mutanen da ambaliyar ya shafa a Najeriya.