AMBALIYA: Gwamnati ta yi watsi da mu a Rimin Gado, jihar Kano

0

Wasu mazauna karamar hukumar Rimin Gado a jihar Kano sun koka kan da rashin kula da gwamnatocin jihar Kano da tarayya suka yi tun bayan fadawa ibtila’in ambaliyar ruwa da mazauna garuruwan yankin suka yi.

Aminu Lawan, da shima ya yi hasara mai yawa ya bayyana cewa tun da hukumar bada agajin gaggawa ta dauki sunayen su da bayanan dukiyoyin da suka rasa babu abin da aka yi musu har yanzu.

Ya kuma ce suna da labarin cewa gwamnatin jihar Kano ta ware Naira miliyan 100 domin agazawa mutanen da ambaliyar ta shafa amma duk da hakan shuru suke ji.

A dalilin haka ne yake kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki domin kuwa suna cikin matsalar gaske a yanzu.

Hukumomin bada agajin gaggawa na jihar Kano da ta tarayya sun bayyan cewa suna nan suna kokarin ganin tallafi ya isa wadannan garuruwa.

Share.

game da Author