ALBASHI: Jihar Jigawa za ta bi tsarin albashin da gwamnoni suka amince da

0

A yau Talata ne gwamnan jihar Jigawa Mohammed Badaru ya bayyana cewa gwamnati za ta yi amfani da amintacciyar tsarin biyan albashin ma’aikata da gwamnonin kasar nan suka amince da shi.

Ya fadi haka ne da yake zantawa da kungiyar kwadago na jihar suka ziyarci gwamnan a fadar gwamnati.

Badarau ya bayyana cewa a yanzu haka gwamnonin kasar nan na tattaunawa da gwamnatin tarayya kan yadda za a sami matsaya daya game da karin albashi da ake shirin yi wa ma’aikata.

A karshe shugaban kungiyar Usman Ya’u da yake jinjina wa gwamnan kan gaggauta biyan albashi, fansho da kudaden sallaman ma’aikata ya yi kira ga Badaru da ya saka baki matuka domin gwamnoni su amince da naira 30,000 karancin albashin ma’aikaci a kasar nan.

Share.

game da Author