ADAMS OSHIOMHOLE: Ruwa Na Neman Kare Wa Dan Kada

0

A yanzu dai ta tabbata cewa saukar da tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, John Odige-Oyegun ya yi a bisa tilas daga shugabancin jam’iyyar ba da son ran sa ba, da nufin a dora Adams Oshiomhole domin ya gyara jam’iyyar kuma ya saisaita ta, ya na neman zama garin gyaran gantsarwa an karya Kwankwaso kenan.

Tun bayan hawan Oshiomhole shugabanci, farkon abin da ya fara yi shi ne kokarin sasanta hasalallun da aka bata wa rai a jam’iyyar, wanda dama aiki ne Shugaba Muhammadu Buhari tun da farko ya dora jigon jam’iyyar, Bola Tinubu ya yi.

Tun ma kafin a zabi Oshiomhole, kusan kowa ya san shi ne zai zama shugaban jam’iyyar, ganin yadda ya ke da daurin gindin Tinubu, wanda ya dauki lokaci ya na ‘yar tsama da Oyegun, har ta kai su ga cacar-baki a kafafen yada labarai.

BA GIRIN-GIRIN BA…..

Duk wani dan APC babba da masu fada a ji, masu mulkin da ke cikin jam’iyyar da kuma kananan magoya bayan jam’iyya har ma da ‘yan ‘Buhariyya Sak’, wadanda Buhari su ke yi kawai ba APC ba, sun rika kallon Oshimhole tamkar wani ‘Mahadin’ da zai gyara rigingimun da suka dabaibaye APC.

Sanata Shehu Sani ya nuna cewa zaman Oshimhole shugaban APC alheri ne ya saukar wa jam’iyyar wanda zai dinke duk wata barakar da ke kokarin farke dinkin rigar APC.

Sai dai me, yayin da ake yaba wa Oshimhole Sallah, sai nan da nan kuma ya kasa alwala. An yi tsammanin hawan sa shugabancin jam’iyya zai kame kai ya zama dattako yadda zai rungumi kowa hannu bibbiyu, tare da sauraren korafe-korafen kowane bangare.

SARTSEN DA OSHIOMHOLE YA FARA YI

Ya hau shugabanci a lokacin da wasu gungun majiya karfin jam’iyyar, wadanda yawancin su daga PDP suka fita suka koma APC, har aka yi nasarar zaben 2015 da su, ke fama da sabani da uwar jam’iyyar gaba daya. Mutane irin su Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, Sanata Rabiu Kwankwaso, Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara da wasu da dama irin sau Sanata Dino Melaye, duk sun samu sabani da uwar jam’iyya, APC.

MAI SASANTAWA YA KOMA HAURAGIYA

Yayin da guguwar da ta tirnike har wasu jiga-jigan cikin jam’iyyar suka fara tunanin ballewa zuwa tsohuwar jam’iyyar su, wato PDP, Oshimhole ya rika bin su gida-gida ya na yi masu magiyar kada su fice, su yi hakuri, za a sasanta lamarin.

Baya ga wannan kuma, ya rika shiga kafafen yada labarai ya na bayyana muhimmancin hasalallun a cikin jam’iyya, wadanda ya rika nuna cewa da taimakon su da kuma goyon bayan su aka kafa gwamnati a 2015.

Sai dai kuma inda biri ya bata rawar sa da tsalle, shi ne, duk wanda ya ki sauraren magiyar Oshimhole ya fice daga jam’iyyar, sai shi shugaban jam’iyyar ya rika bin sa da bakaken kalamai a kafafen yada labarai.

Ya rika kiran wanda ya fita da sunan karan-kada-miya, wani ya kira shi wanda ba bakin komai ba, wasu kuma ya kira su gungun banza-bakwai, wasu kuma ya ce da su da babu duk daya.

TALLE NA YI WA AUDI GORI?

Oshimhole ya rika wuce gona da iri ya rika kiran wasu da suka fice daga APC da cewa dama duk garken barayi ne, wadanda su ka ga cewa ba su da halin da za su balle murfinn kofar kudi shiga su rika kamfata kamar yadda aka yi a mulkin PDP, shi ya sa suka fice daga APC.

Oshiomhole, wanda shi ma akwai igiyar zargin wawurar makudan bilyoyin kudade a kan sa a zamanin da ya yi gwamna jihar Edo shekara 8, tsakanin 2008 zuwa 2016, har yanzu ya na ta kai gwauro ya na kai mari ya na neman kotu ta hana EFCC binciken sa.

Tun da farko dama wani dan Jihar Edo ne ya kai kwafen takardun korafi da kuma kwafen takardun hujjojin da ke nuna cewa Oshimhole ya cika aljifan sa fal da dukiyar jihar Edo, amma EFCC ba ta yi komai a kai ba.

Mutumin ya hasala, ya kai kara kotu, inda kotu ta umarci EFCC ta kama Oshimhole ta bincike shi sannan kuma ta gurfanar da shi a kotu. A nan ma Oshimhole ya sake garzayawa kotu domin ya hana a bincike shi.

RAWAR OSHIOMHOLE A ZABEN FIDDA GWANI

Zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da aka kammala a kasa baki daya, ya wuce, amma fa ya bar baya da kurar da ta tirnike jam’iyyar har ta kai ga shake ta. Ana itttifakin cewa tun da aka fara siyasa a Najeriya, ba a taba yin zaben fidda gwanin jam’iyya da aka yi harigido da kwamacala da barankyankyama kamar na APC a fadin kasar nan ba, kuma a karkashin sa-idon Oshiomhole.

Da farko jam’iyyar ta bi ka’idar da dokar da ta gindaya a zaben fidda gwani, inda ta nuna cewa za a iya yin zaben a karkashin zabe ta hanyar yin amfani da wakilan zabe na jam’iyya, wato ‘delegates’, ko kuma a yi kato-bayan-kato, watau ‘yar tinke.

Daga inda aka fara samun tankiya shi ne inda a jihohi akasari, wakilan zabe wato delegates, duk na gwamna mai ci ne, wanda hakan ke nuni da cewa idan ba wanda gwamna ke so ba, to babu yadda za a yi wani dan takara ya yi nasara.

Matsala ta biyu kuma it ace, duk inda aka ce a yi zaben kato-bayan-kato, to akasari jama’a ba su son wanda za a dora musu, shi ya sa suke jajirce a a yi kato bayan bayan kato.

Ko ma dai me kenan, an gudanar da zabukan fidda gwani kala biyu, kuma sun wuce, amma sun haifar da ragarimar rigima a cikin jam’iyyar.

Da yawa sun zargi Oshiomhole da hannu wajen dagula al’amurra. Shugaban Gidan Radiyon Muryar Najeriya, Osita Okechukwu ya kira Oshimhole da sunan dan damfara.

Gwamna Okerelolu na Ondo ya kira shi dan jagaliya, yayin da Gwamna Amosun na jIhar Ogun ya kira shi dan gada-gada.

Jarida Sahara Reporters ta buga wani labari na musamman a jiya Laraba, inda ta bayyana yadda aka rika zargin Oshimhole da mukarraban sa Shugabnnin Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar APC suka rika karbar daga naira milyan 10 har zuwa naira milyan 50 daga hannun ‘yan takara a fadin kasar nan, su na canja sunayen wasu da ba ‘yan gaban-goshi ba, su na maye gurbin su da wadanda ba su yi nasara ba.

A fili ta ke cewa APC ta rikice kuma ta rude a jihohi da yawa sakamakon harigidon da aka yi a zaben fidda-gwani.

Yayin da INEC ta ce APC ba za ta tsaya takara a jihar Zamfara ba, haka kuma wani hukunci da Kotun Koli ta yanke a ranar Litinin na nuni da cewa da wahalar gaske jam’iyyar ta tsaida ‘yan takara a jihar Ribas.

Sannan kuma har zuwa yau, Kakakin Yada Labaran APC, Lanre Issa ya bayyana cewa har yanzu ba su da dan takarar gwamna a jihar Imo.

A Imo dai Gwamna Rochas Okorocha ne ya tsaida sirikin sa a matsayin dan takarar gwamnan da zai gaje shi. Hakan ne ya sa mutane irin su Osita Okechukwu suka maka jam’iyyar da gwamnan kara kotu.

OSHIOMHOLE: DAN KUKA MAI JA WA UWAR SA JIFA

Harkalla da cuwa-cuwar da wadanda suka yi zargin an yi a fadin kasar nan, yayin zaben fidda-gwanin APC, ya hasala da dama daga cikin gwamnoni, sanatoci, wakilan tarayya da na jihohi da kuma sabbin-yanka-raken shiga takara, wadanda suka yi korafin cewa an sa sun kashe milyoyin kudade sun yanki fam, sun kashe kudade wajen yakin neman zabe, amma daga bisani an tafka musu magudi an canja sunayen su da sunayen wasu.

A jihar Adamawa wani dan takarar sanata mai suna Idris ya bada labarin yadda ba a yi zabe ba amma aka ce an yi zabe. Ya ce sun sha wahala, ya daukin tsawon lokaci ya na shiri, ya kashe sama da naira milyan 150, amma kwanaki biyu kafin zabe Binta Garba Masi ta fito takara, na a ma yi zaben ba, amma aka ce wai ita ce ta yi nasara.

Dan takarar ya hasala a wurin taron sasantawa har ya rika surfa mata zagi, ya mike ya nemi zabga mata mari a tsakiyar jama’a. Idris y ace zain ga yadda APC za ta ci zabe a karkashin wannan turba ta rashin adalci.

Ire-iren wadannan hasalallun sun rika dora laifin rincabewar zaben a kan Shugaba Muhammadu Buhari, wanda su ka ce duk rigimar da ta taso, muddin ba ta shafi kujerar sa ba, to babu ruwan sa.

Hususan sun kafa hujja da yadda ya fito ya bayyana cewa dukkan wadanda aka bata wa rai a zaben fidda gwani, to ya dauki kaddara kuma ya danne zuciyar sa, kada ya yi fushi har ya fice daga jam’iyyar.

Dama kuma idan ba a manta ba, a zaben shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar cikin watan Yuni da Yili, an tafka mgudi kuma ya haifar da rudani. Maimakon Buhari ya dauki mataki, sai ya furta cewa an yi kurakurai, amma a yi hakuri a tari gaba.

KARYAR KWARAM-KWARAM TA KARE

A halin da ake yanzu, masu kiran a tsige Oshiomhole sai kara yawa suke yi, kuma sai kara fitowa fili suke yi su na ci gaba da busa begilar neman a cire shi.

Da yawa na ganin matsawar aka ce ya na shugabanci za a yi zaben 2019, to APC za ta kwashi buhun kunya a jihohi da dama.

Wasu ma na ganin matsawar aka ce shi ne shugaba har lokacin zabe, to shakka babu da yawan wadanda aka bata wa rai za su kasance ba su da wani zabi a ranar zabe, sai na yi wa APC zagon-kasa, abin da a Turance ake cewa ‘Anti Party.’

OSHIOMHOLE: KITSEN ZAKI KO KITSEN ROGO?

Wane tasiri Oshiomhole zai kara yi a APC idan ya ci gaba da rike jam’iyyar? Wane rikici zai iya warwarewa a yanzu ko a nan gaba? Ko kuwa dama kallon kitse a ke wa rogo a jikin Oshiomhole kafin APC ta zabe shi shugaban ta? Wannan fa shi ne ‘karyar kwaram-kwaram ta kare, wai mai kalangu ya fada ruwa.’

Gwamna Akeredolu dai ya ce dama can bai iya shugabanci ko jagorancin jama’a ba, dan jagaliya ne kawai, wanda ya shigo ya damalmala wa APC lissafi, yadda har ta kai tunanin cin zaben 2019 da jam’iyyar ke yi, sai an hada da ‘addu’a’, ko kuma a rufe ido a tsige Oshimhole, idan ba haka ba kuwa, PDP za ta iya tsige su gaba daya.

Dabara ta rage wa mai shiga rijiya!
Sanata Shehu Sani ya fi dacewa ya bayyana ko wane ne Oshimhole a halin yanzu. Domin shi ne a ranar da aka zabe shi shugabancin jam’iyya, y ace Oshiomhole alheri ne. Amma kuma a ranar Litinin da ta gabata, Sani ya furta cewa duk mutumin kirki da kuma dattijon kwarai da ya san darajar gemun sa, ba zai ci gaba da zama cikin APC ba.

Share.

game da Author