A karon farko gwamnati ta yi magana kan rikicin NHIS

0

A karon farko gwamnatin tarayya ta yi magana game da rikita-rikitan da ya dabaibaye shugaban hukumar Inshorar lafiya ta Kasa Yusuf Usman da ma’aikatan hukumar.

Da yake hira da gidan talabijin din Channels, Lai ya ce gwamnati na sane da abin da yake faruwa a hukumar kuma tabbas za ta kawo karshen abin nan ba da dade wa ba.

Idan ba a manta ba hukumar ta samu kanta ne cikin kamayamayar shugabanci tun bayan kwamitin gudanarwar hukumar ta dakatar da shugaban hukumar bisa zargin yin sama da fadi da kudaden hukumar.

Sai dai kuma tun bayan sanar da dakatar da Yusuf aka shiga kai ruwa rana tsakanin masu goyon sa da kungiyar ma’aikatan da suka lashi takobin sai ya ajiye aikin na sa an gudanar da bincike a kai.

Hakan ya sa a makon jiya Yusuf tare da jami’an ‘yan sanda 50 suka tarwatsa gungun ma’aikatan da suka yi cincirundo a ofishin suka ce lallai ba zai wuce ya shiga ofis ba

Tun daga wannan rana dai hukumar ta kasa tsaye ta kasa tsugune, a kullum sai kaji sabon hayani iri-iri.

Yusuf ya ce babu wanda ya isa ta hana shi zuwa auki domin doka bata ba kwamitin gudanarwar hukumar ikon dakatar da shi ba.

Share.

game da Author