2019: Zaben Atiku maida hannun agogo baya ne – Lai Mohammed

0

Ministan yada labarai Lai Mohammed ya gargadi yan Najeriya da su tattaro hankulan wuri daya su yi karatun ta natsu a zaben da tafe.

Lai Mohammed ya bayyana cewa tabbas zaben Atiku Abubakar, shugaban kasar nan maida hannun agogo baya ne.

” Bayan an kokarta an sammu an dan kubuta daga harkallar watandan kudin kasa, sai kuma ace kasa Najeriya ta koma wannan tsari.

” Su kan su yan Najeriya sun san ciwon kan su. Zaben Buhari ne mafi Alheri ba wanin da ba haka ba.”

Lai Mohammed fadi haka ne da yake amsa tambayoyin manema labarai da ya kai ziyara gidan Talabijin din AIT a garin Abuja.

Idan ba a manta ba tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ne ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a garin Fatakol ranar Asabar.

Hakan ya nuna cewa shine dan takarar da zai yi fafata da Buhari da sauran ‘yan takarar wasu jam’iyyun.

Share.

game da Author