2019: Gara dubun Buhari da Atiku daya – Inji Balarabe Musa

0

Shugaban kwamitin aminttattu na Jam’iyyar PRP, kuma tsohon gwamnan jihar Kaduna Balarabe Musa ya gargadi ‘yan Najeriya da su shiga taitayin su, kada su kuskura su maye shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar.

Balarabe Musa ya bayyana haka ne da yake hira da PREMIUM TIMES a Kaduna.

Musa ya ce duk da cewa Buhari bai tabuka komai ba a tsawon mulkin sa, ba Atiku bane ya kamaci a musanya shi da.

” Eh Buhari bai tabuka komai ba amma Atiku ya fishi zama hadari ga kasar nan. Duk wadanda suke tare da Atiku mutane ne da suka yagalgala Najeriya a baya kuma sune zasu ci gaba idan ya dare kujerar mulki.

” Atiku hamshakin attajiri ne kuma yana da mutane masu karfin arzikin gaske da ke tare da shi. Babu wanda zai iya juya shi yadda yake so sannan ba a isa ace masa tak ba ganin irin karfin arziki da ya ke da shi da goyon bayan tsoffin shugabannin kasar nan da yake da.

” Za a fi iya fafatawa da Buhari fiye da Atiku kuma a samu daidaituwa komai kankantar abin fiye da idan Atiku ne a wannan kujera.

Balarabe Musa ya ce yana ba ‘yan Najeriya shawara da su zabi Buhari maimakon Atiku duk da lalacewar mulkin Buhari.

Share.

game da Author