Tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo na ganawar sirri da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda shine mataimakin sa a wancan lokaci.
A tawagar Atiku akwai shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus da jagorar kamfen din Atiku, Gbenga Daniel.
Zuwa yanzu ba a sami cikakken bayani kan dalilin wannan ziyara ba sai dai kuma ziyarar na da nasaba da shirin zaben 2019.
Idan ba a manta Atiku Abubakar ne ya lkashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP in da ya doke abokanan takarar sa su 11.
Atiku ne zai cira tutar jam’iyyar PDP din a zaben 2019 in zai fafata da shugaban kasa mai ci wato Muhammadu Buhari.