2019: APC ta jaddada cewa INEC za ta gudanar da sahihin zabe

0

Jam’iyyar APC ta jaddada yakinin ta na cewa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), za ta gudanar da zabe mai inganci kuma sahihi a 2019.

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Riko, na Shiyyar Kudu, Niyi Adebayo ne ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Kungiyar Tarayyar Turai a Abuja a jiya Litinin.

Tawagar ta na a karkashin jagorancin Nicolay Paus.

Adebayo wanda ya bayyana wa tagawar cewa jam’iyyar APC ta shirya wa zaben, ya kuma kara da cewa ya na da yakinin kotuna da alkalai za su iya warware duk wata tankiyar da za ta iya tasowa kafin ko bayan an gudanar da zabe.

Daga nan sai ya gode wa Kungiyar Tarayyar Turai (EU), bisa daukar tsawon lokacin da ta yi wajen nuna goyon bayan habbakawa da inganta tsare-tsaren zabe a Najeriya.

Tun da farko, Nicolay Paus ya shaida cewa tawagar sa ta gana da masu ruwa da tsaki wajen zabe, ciki har da IINEC, jam’iyyun siyasa da kuma Ma’aikatar Harkokin Kasashen Waje.

Ya kuma ce sun gana da kungiyoyin kare hakkin jama’a na cikin kasar nan da kuma na kasa-da-kasa masu gudanar da ayyukan taimaka wa sha’anin gudanar da zabe.

Ya ce ganawar ta na da nasaba ne da ko akwai yiwuwar kungiyar ta EU za ta iya turo tawagar sa-ido domin ganin yadda za a gudanar da zaben 2019 a Najeriya.

Share.

game da Author