Za a yi Gasar Sarauniyar Kyau ta matan aure a Abuja

0

Ranar 21 Ga Oktoba ne za a gudanar da Gasar Sarauniyar Kyau ta matan aure a jihar Legas. Wannan gasa wadda za a gudanar a karo na biyu, an fara gudanar da ita ce a cikin 2017.

Masu gudanar da gasar za su zabi kyawawan matan da za su yi gasar a tsakanin matan auren da duka kai shekara 23 zuwa masu shekara 45.

Jakadiyar shirya gasar a karkashin kamfanin Pageants Nigeria Limited, sun bayyana haka a Lagos, inda suka ce duk wadda za ta shiga gasar, to ta kasance matar aure ce, mai wata sana’ar cin gashin kanta, ko wani aikin dogaro da kai, ko kwararriya a wani fanni.

Sannan kuma ta kasance ta na da aure, kuma idan ta taba haihuwa, to hakan karin yiwuwar samun nasara ce a wurin ta.

Ba a yarda ‘yan mata da ba su da aure, ko kilakai ko masu yawon-ta-zubar su shiga gasar ba.

Wadda ta lashe gasar farko da aka shirya cikin 2017, mai suna Faith Ogaga, matar aure ce mai ‘ya’ya biyu, kuma ita ce ta wakilci Najeriya a gasar Sarauniyar Kyau ta Matan Auren Duniya da aka gudanar a Afrika ta Kudu, cikin 2017.

Jakadiyar shirya gasar, Sarah Awogwui ta shaida kamar yadda PREMIUM TIMES ta ruwaito a ranar Laraba a Lagos cewa wannan gasa ta na tallafa wa mata ne musamman wajen ci gaban al’umma da kuma kulawa da inganta rayuwar kananan yara.

Share.

game da Author