2019: Atiku ya zabe Peter Obi mataimakin dan takarar shugaban kasa

0

Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi ganawar sirri tare da Peter Obi, kamar yadda Premium Times tabbatar.

Obi ya isa gidan Atiku da ke Asokoro, Abuja, da misalin karfe 3 na yamma a yau Juma’a, kuma suka gana a gaban masu daukar bidiyo da hutuna.

Ana kwakkaran rade-radin cewa Atiku zai dauki Peter Obi ne a matsayin mataimakin shugaban kasa a takarar da zai yi karkashin PDP.

Majiya da dama masu kusanci da Atiku, sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya zabi Obi a matsayin mataimakin sa na takara bayan kammala taron na su.

Wata majiya kuma ta ce Asabar da safe ne za a sanar da Obi a matsayin dan takara.

Tun bayan da aka zabi Atiku ake ta ji-ta-ji-tar wanda zai dauka a matsayin mataimakin sa na takara, ko dai a yankin kudu maso yamma na Yarbawa ko kuma Kudu maso gabas a cikin kabilar Igbo.

Amma yanzu zabin da ya yi wa Obi, ana sa ran zai iya janyo masa dimbin magoya baya a Kudu Maso Gabas.

Obi ya yi gwamnan jihar Anambra tsakanin 2006 da kuma 2014 a karkashin jam’iyyar APGA.

Duk da cewa ba a sanar da daukar Obi da Atiku ya yi ba, tuni Sanata Ben Bruce ya taya Obi din murna a shafin sa na twitter.

Bruce na daya daga cikin na hannun damar Atiku.

Share.

game da Author