Taron dRPC: Kashi 11 ne kacal na mata a Najeriya ke amfani da dabarun bada tazarar iyali – Bincike

0

A yau Alhamis ne cibiyar ‘Development Research and Project Centre (dRPC)’ ta shirya taro domin tattauna hanyoyin bunkasa amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.

An gudanar da wannan taro ne a Abuja inda ma’aikatar kiwon lafiya, masu fada a ji a fannin kiwon lafiya da wakilan gwamnati suka halarci wannan taro.

Jami’in dRPC Emmanuel Abanida ya bayyana cewa har yanzu dai mutane musamman mata na gudun amfani da dabarun bada tazarar iyali a Najeriya.

Abanida ya ce bincike ya nuna cewa kashi 11 bisa 100 na mata a Najeriya ne kacal ke amfani da dabarun.

Ya ce kamata ya yi mutane su gane cewa amfani da dabarar bada tazaran iyali hanya ce dake taimakawa wajen inganta kiwon lafiyar mace da na yara.

” Ya zama dole fannin kiwon lafiya tare da masu fada a ji a fanin su zage damtse wajen ganin an wayar da kan mutane game da mahimmancin amfani da dabarun bada tazaran iyali.

Bayan haka jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na Kasa, Kayode Afolabi ya bayyana cewa babbar matsalar dake hana samun ci gaba da kuma karancin masu yin amfani da dabarun bada tazarar Iyali shine talauci da yayi wa mutane katutu.

Ya ce a yanzu haka kungiyoyin bada tallafi kamar su gidauniyyar Bill da Melinda Gates, babban bankin duniya sun bayyana cewa asibitocin gwamnati a kasar nan na bada dabarun bada tazarar iyali kyauta duk da haka ta yi kira da a samar da kudade na musamman domin haka.

” Gwamnatin kasar nan ta ware kasha 4 bisa 100 cikin kassafin kudin kasar nan domin fannin kiwon lafiya wanda hakan ba zai kai ko’ina ba sannan gwamnati ba ta cika wasu alkawurorin da ta dauka domin inganta kiwon lafiyar Najeriya.

A dalilin haka Afolabi yake kira ga gwamnati ta maida hankali wajen bunkasa fannin kiwon lafiya tanajin kudaden masu tsoka domin hake na kawai mafita ga matsalolin da ake fana dasu.

Share.

game da Author