A daina yanke hukuncin kisa a duniya – Shugaban UN

0

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteres, ya yi kira da a soke yankewa da kaddamar wa masu laifi hukuncin kisa a duniya.

Gutteres yayi wannan kira ne a cikin wani jawabi da ya fitar a Ranar Zagayoyar Yaki da Hukuncin Kisa ta 16, tare nuna damuwar cewa kakkafe hukuncin kisa a duniya ya hadu cikasa sosai.

Ya yi tsokacin cewa daruruwan masu laifi wadanda ba su da karfi da abinci, mafi yawa kuma mata, ana yanke musu hukuncin kisa ba tare da samun wakilci ko daukar lauya ba.

Ya nuna cewa watakila yawancin su da a ce sun samu lauyoyin da za su kare su, to da ba a yanke musu hukuncin kisan ba.

Wasu kasashe 170 sun soke hukuncin kisa, ko kuma sun dakatar da kashe wasu da aka yanke wa hukuncin kisa, tun bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a soke hukuncin cikin 2007.

Ya kuma nuna takaicin yadda ake yawan yanke wa kananan yara hukuncin kisa a wasu kasashen.
Daga nan sai ya yi kira ga sauran tsirarun kasashen da ake yanke hukuncin kisa har yanzu da su soke hukuncin gaba daya.

Ya yi nuni da cewa akasarin kasashen da suka fi aiwatar da hukuncin kisa a yanzu sun hada China, Pakistan, Iraq, Iran da Saudi Arabiya.

Share.

game da Author