Wasu likitoci a jami’ar Harvard dake Boston kasar Amurka sun bayyana cewa shan maganin ‘Aspirin’ na kare mace daga kamuwa da cutar dajin dake kama mahaifa.
Likitocin sun gano haka ne a bincike da suka gudanar inda suka gano cewa mace kan samu kariya ne idan ta na shan wannan maganin kasa da yawan da ya kamata a sha.
Dama likita kan bada Izinin a sha miligaram 325 na wannan maganin amma samun kariya daga wannan cutar shine idan an sha miligaram 100.
” Bisa ga binciken da suka gudanar matan da suka sha miligaram 100 na wannan maganin sun samu kashi 23 bisa 100 na kariya daga kamuwa da wannan cutar fiye da matan da basu sha wannan magani kwata-kwata ba.
Discussion about this post