A cikin watanni biyu mutane 10,315 sun kamu da zazzabin cizon sauro a Jigawa

0

A yau Talata ne shugaban hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na jihar Jigawa (JPHCDA) Yusuf Hakimi ya bayyana cewa a tsakanin watannin Agusta da Satumba 2018 mutane 10,315 sun kamu da zazzabin cizon sauro a jihar.

Ya fadi haka ne a garin Hadejia da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya.

Hakimi ya bayyana cewa an samu wannan adadi ne sakamakon bincike da suka yi a cibiyoyin kiwon lafiya dake jihar.

” Babbar matsalar da yake kawo irin wannan cuta a yankunan mu sun hada da rashin tsaftace muhalli da ba a yi. Magudanar ruwa duk sun ciccike wanda hakan ke sa sauro ya yawaita.

Daga nan sai yayi kira ga mutane da su tsaftace muhallin su sannan su rike bude magudanan ruwa domin kare kai daga irin wadannan matsaloli.

Share.

game da Author