Akalla Jarirai 11,455 ne ke mutuwa duk shekara a jihar Bauchi – BINCIKEN UNICEF

0

Jami’in asusun tallafa wa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) Oluseyi Olusunde ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukan mataki wajen ganin an rage yawan mace-macen jarirai a jihar Bauchi.

Olusunde ya fadi haka a taron tattaunawa da UNICEF, EU, Gwamnatin jihar da sauran ma’aikatan kiwon lafiya suka yi a jihar domin shawo kan mace-macen jarirai a jihar.

Ya ce bincike ya nuna cewa a cikin jarirai 1000 da ake haihuwa a jihar akalla 161 na rasuwa kafin su kai shekara biyar. Sannan a shekara kuwa jihar kan rasa jarirai 11455.

Wanda hakan ke nuna cewa jihar Bauchi ita ce ta biyar cikin jihohin Najeriya dake fama da wannan matsala.

Olusunde ya bayyana cewa gwamnati ta kafa kwamiti mai suna ‘Bauchi State Every Newborn Action Committee (BASENAC)’ domin tsaro kudirorin da za su taimaka wajen rage mace-macen jarirai a jihar.

Bayan haka wani jami’in UNICEF Bahanu Pathak ya ce akwai wasu matsaloli da ya kamata gwamnati ta shawo kan su game da mutuwan jarirai a jihar wanda hakan ya sa UNICEF ta amince ta hada hannu da gwamnati domin kawar da wadannan matsaloli.

A karshe shugaban kwamitin BASENAC Rabinson Yusuf ya ce gwamnati za ta maida hankali wajen ganin an kawo karshen wannan matsala da ake fama da shi a jihar.

Share.

game da Author