APC: Ina taya wadanda suka yi nasara a zabukkan murna – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga daukacin ‘yan jam’iyyar APC da suka yi nasarar zaben fidda gwani da aka kammala jiya Lahadi, ya na kuma rokon wadanda ba su yi nasara ba da su dauki kaddara.

Buhari ya kara yin kira a gare su kada su maida siyasa wata sana’a mai daci kamar madaci, kuma kada su riki wadanda suka kayar da su da kiyayya a zuciya ko a sarari.

“Ita dama gasa haka ta ke, a kowace gasa ana samun wanda zai yi nasara da wanda aai fadi, amma dai su wadanda suka fadi, kada su fusata su fice daga jam’iyyar, kuma kada so da kaunar jam’iyyar ya dusashe daga zukatan su”

Buhari ya roki duk wanda bai yi nasara ba da ya yi koyi da mutane irin gwamnan Jihar Lagos, Akinwunmi Ambode, “wanda duk da cewa ya fadi zabe, bai fusata ya fice daga jam’iyyar APC ba domin ya samu tutar sake tsayawa takarar gwamna a can.”

Buhari ya kara da cewa: “muhimmancin da tasirin jam’iyyarmu ya fi muhimmanci da tasirin buri ko son zuciyar kowane dayan mu. Don haka ina kira mu hada kai mu yi wa jam’iyya aiki, ko da kuwa mutum ya fadi a zaben fidda-gwani.”

Shugaba Buhari ya kara da cewa, “a siyasa mutum ba ya sarewa har ya yanke kauna daga samun nasara, domin idan yau ba ka samu ba, gobe na nan zuwa, sai ka ga wata dama ta samu har kai ne ka yi nasara.”

Share.

game da Author