Buhari bai umarci El-Rufai ya hukunta Shehu Sani ba – Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar shugaban kasa ta karyata wata wasika da ake ta yadawa a kafafen yada labarai wai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya hukunta sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani.

Sannan kuma wai gwamnan ya hukunta duk wadanda suka yi wa jam’iyyar yankan baya.

Sai dai kuma hakan bai yi wa fadar shugaban kasa dadi ba domin a sanarwar da kakakin ofishin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, ya yi kira ga mutane da gidajen yada labarai da su yi watsi da wannan takarda cewa bai fito daga ofishin Buhari ba.

” Duk wanda ya san Shugaba Buhari ba zai umarci wani ya hukunta dan jam’iyya ba, bayan kuwa wannan hakki ne na uwar jam’iyya. Saboda haka a yi watsi da wannan takarda domin Buhari bai san da ita ba.” Inji Garba Shehu.

Idan dai ba a manta ba tun bayan da jam’iyyar APC ta fitar da sunayen Sanatocin da ta amince su cira mata tuta a zabe mai zuwa, aka samu rudani a jam’iyyar reshen jihar Kaduna.

A wannan jerin sunaye babu sunan mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani wanda shima dan takara ne na jam’iyyar da wasu.

Uwar jam’iyya dai ta ci gaba da nanatawa cewa Sanata Shehu Sani ne dan takarar ta. Amma kuma duk da haka sai da aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar a jihar ranar Asabar.

Sakamakon zaben ya nuna cewa Uba sani ne ya lashe zaben da kuri’u sama da 2000 in da sanata Shehu Sani ya sami kuri’u 15.

Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta ne mi ji daga bakin kakakin jam’iyyar Yekini Nebena, ya sake fitowa karara in da ya bayyana wa jam’iyyar cewa dan takarar jam’iyyar da ta amince da shine Sanata Shehu Sani.

Share.

game da Author