Tun bayan da aka bayyana nasarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya samu a zaben fidda dan takarar jam’iyyar PDP, ‘yan takara da magoya baya suka yi ta kwararo sakon ta ya murna bisa nasarar da ya samu a zaben.
Wasu daga cikin ‘yan takarar da suka fafata da da Atiku sun yabawa jam’iyyar kan yadda aka gudanar da zaben a Fatakol.
” Yanzu za mu dawo ne gabadayan mu mu mara wa dan takarar mu baya. Abin da ke gaban mu shine mu hadu mu kau da jam’iyyar APC da Buhari a 2019.” Inji Saraki
Haka shima gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo ya bayyana cewa zasu hada karfi da karfe wajen ganin jam’iyyar PDP da dan takarar jam’iyyar ya samu nasara a zaben 2019.
Sai dai kuma jim kadan bayan an bayyana sakamakon zaben, sai gwamnan Ribas Nyesom Wike ya fice daga filin taron ganin cewa gwanin sa, wato gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal bai lashe zaben ba.