A ranar Asabar ne jam’iyyar reshen jihar Kaduna ta gudanar da zaben fidda dan takarar kujerar sanata ta shiyyoyi Uku dake jihar.
A Kaduna ta tsakiya, da ake ta takun saka tsakanin dan takarar kujerar, Shehu Sani da uwar jam’iyyar ta wanke da sauran ‘yan takara abin dai ya canja zani ne bayan samun amincewar jam’iyyar da ayi zaben fidda gwani na shiyyar.
A zaben da aka yi wanda hukumar zabe da kanta ta shaida ya nuna cewa Mal Uba Sani ne ya lashe zaben da kuri’u sama da 2000, sannan shi kuma Shehu Sani da shine wanda ya ke kan kujerar ya samu kuri’u 15 ne kacal.
A shiyyar Kaduna ta Kudu kuwa mataimakin gwamnan jihar Barnabas Bantex ne ya lashe kujerar.
Sai dai kuma akwai sauran rina a kaba, domin har yanzu uwar jam’iyyar ta hakikance cewa Sanata Shehu Sani ne dan takaran ta.
Amma kuma kamar yadda doka ta shar’anta shine wadda aka yi aka kuma fidda sakamako. Amma kuma jam’iyya ce ke da ikon fadin wanene zai cira mata tuta.
Discussion about this post