ZAWARAWAN PDP 12: Wanene Ba Wanene ba, Atikun ne ko Kwankwaso, Sarakin ne ko Tambuwal?

0

A yau Asabar ne za a yi ta ta kare a Fatakwal, babban birnin Jihar Rivers, inda daukacin jiga-jigai da magoya bayan jam’iyyar PDP ke ta tururuwa domin gudanar da taron gangamin jam’iyyar na kasa, inda za su zabi dan takarar shugaban kasa, wanda zai kafsa da Shugaba Muhammadu Buhari na APC, a zaben 2019.

Ba shakka PDP ta dauka babbar damarar kokawa sosai, sai dai kuma duk da haka, idan aka dubi yawan ‘yan takarar har su 12, wasu na ganin cewa kamar sun yi yawa.

Ganin har wayewar garin yau Asabar ba a ji batun cewa za a fitar da dan takara daya tilo ba tare da sai an kada kuri’a ba, hakan ya nuna cewa kenan za a yi zabe domin wakilai su zabi na zabe.

Akalla akwai masu zabe kimanin 4,000 da za su kada kuri’a domin a fitar da gwanin da su ke ganin zai iya kayar da Buhari na jam’iyyar APC a zaben 2019 mai zuwa.

PREMIUM TIMES ta dan tsakuro kadan daga ‘yan takarar domin a fahimci yiwuwa ko rashin yiwuwar nasarar kowane.

ATIKU ABUBAKAR:

TASIRIN SA: Atiku tsohon Mataimakin Shugaban Kasa ne na tsawon shekaru takwas. Ya tsaya takara a baya, kuma ya saba da gwagwarmaya. Ya na da jama’a kuma ya san logar siyasa da mulki. Kasaitaccen attajiri ne, dan kasuwa kuma manomi. Ya na a sahun gaba na wanda ya fi sauran daukar ma’aikatan da ke karbar albashi duk wata a karkashin sa. A cikin 2013 ya ce ya akwai ma’aikata kusan 50,000 a kamfanonin sa daban-daban.

CIKAS: Atiku ya sha fita daga PDP ya na komawa. Wasu na ganin cewa yawan shekarun sa zai sa a fi karkata a sabbin jini, irin su Aminu Tambuwal ko Ibrahim Dankwambo.

AHMED MAKARFI:

TASIRIN SA: Ya taba yin gwamna daga 1999-2007 a Jihar Kaduna. Kuma tun da ya shiga PDP bai taba fita ba. Tsohon Sanata ne wanda ya taba yin shugabancin rikon-kwarya na PDP. Wannan ka iya ba shi samun magoya baya sosai.

CIKAS: Matsalar Ahmed Makarfi ita ce duk da shugabancin jam’iyyar da ya taba yi, ba shi da jama’a kamar irin Atiku, Lamido ko Rabi’u Kwankwaso. Amma dai ba a nan ta ke ba.

AMINU TAMBUWAL:

TASIRIN SA: Ana yi masa kallon ‘na kawo karfi, ya fi an girme ni.’ Tambuwal ya na da magoya baya musamman a cikin mambobin majalisar tarayya, inda ya taba yin shugabanci na tsawon shekara hudu. Ya saba kuma ya san gwagwarmayar mulki na siyasa. Ya kuma sa samun goyon baya a duk lokacin da rikici ya taso tsakanin bangaren gwamnati da na majalisa, a lokacin da ya na kakakin majalisar tarayya. Tasirin Tambuwal a matsayin wanda bai kai shekarun wasu ‘yan takarar ba, zai iya sa ya samu nasara.

CIKAS: Wasu ya zu iya yi masa kallon ‘raina kama’, wato a ga cewa kamar bai goge sosai ba ko kuma wasu gagga irin su Atiku da Saraki su yaji babban kaso daga cikin jama’ar Tambuwal. Musamman tsoffi da sabbin ‘yan majalia.

SULE LAMIDO:

TSAIRIN SA: Ya yi gwamna a Jihar Jigawa, kuma a lokacin sa ne babban birnin jihar, Dutse ya sauya daga mataccen gari zuwa mashahurin birni. Ya yi ayyuka masu dimbin yawan da za a dade ba a samu gwamnan da ya kwatanta kamar sa ba. Lamido ya fi sauran ‘yan takara biyayya ga jam’iyya, kuma ya fi kowa dadewa a cikin PDP, domin da shi aka kafa jam’iyyar, sannan kuma ya riga sauran ‘yan takara fara fitowa fili ya nemi fitowa takarar shugabancin kasar nan, a karkashin PDP.

CIKAS: Cikas din Lamido shi ne yadda ‘yan takara suka fito dafifi kowa na so. Amma idan ana duba cancanta, to ya cancanci zama dan takarar PDP. Sai dai kuma Saraki da Tambuwal ka iya fin sa magoya baya a cikin tsoffi da sabbin ‘yan majalisar tarayya.

RABIU KWANKWASO:

TASIRIN SA: Tsohon gwamna ne na jihar Kano sau biyu, kuma ya yi mataimakin kakakin majalisar tarayya a baya. Kwankwaso mutum ne mai dimbin magoya baya a Arewacin kasar nan. Guguwar akidar siyasar sa ta ‘Kwankwasiyya’ ta bugawa ko’ina. An shaida yadda aka yi gwagwagwa da shi a zaben fidsa-gwani na APC a 2014, inda ya zo ba biyu bayan Buhari da kuri’u sama da 3,000. Kwankwaso gogaggen dan siyasa ne.

CIKAS: Cikas din Kwankwaso shi ne yawan ‘yan takarar da su ka fito kafsawa tare da shi. Sannan kuma ana yi masa fahimtar cewa mutum ne mai taurin kai, da bai jin shawara, da wuya ‘yan ba-ni-na-iya su iya tankwasa shi.

BUKOLA SARAKI:

TASIRIN SA: Tsohon gwamnan jihar Kwara ne, kuma ba wannan ne karon farko da ya fara fitowa takarar shugaban kasa ba. Gogaggen dan siyasa ne, tunda yanzu ya zame wa jam’iyyar APC mai mulki karfen kafa, kasancewar sa shugaban majalisar dattawa. Ya na da karfin jama’a a cikin tsoffi da sabbin sanatoci. Zai iya kai Labara ko kuma a tsare masa da kyar da gumin goshi.

CIKAS: Cikas din Saraki shi ne rigingimu sun yi yawa a kan sa. ya zama karo da goma kalacin safe. watakila masu zabe su guje shi gudun kada jam’iyyar APC da magoya bayan ta su rika ruruta rigingimun da ke kan Saraki har su janyo masa cikas idan ma aka tsayar da shi takara.

IBRAHIM DANKWAMBO:

TASIRIN SA: Dankwambo ya nuna jarumtaka a zaben 2015, yadda duk irin karfin guguwar Buhariyya a Arewacin kasar nan, ba ta gaggabe bishiyar gwamnatin sa ba a jihar Gombe. Shi kadai ne gwamnan da ya ci zabe kaf a Arewa a karkashin APC, idan ka fidda jihar Taraba. Sannan kuma tunda ba shi da matsanancin shekaru da dama, wannan zai iya zama tasiri a wurin sa, tunda ga shi kuma ya san mulki, kuma ya san cukumurdar hada-hadar kudaden gwamnati, a matsayin sa na tsohon akanta janar na tarayya.

CIKAS: Cikas din sa shi ne da ya ke su biyu ne gwamnonin da ke neman shugabancin kasar nan, shi da Tambuwal, za a iya cewa Tambuwal ya fi shi kusanci da masu fada-a-ji na jam’iyyar PDP, kuma ya fi shi kusanci da tsoffi da sabbin ‘yan majalisar tarayya.

DATTI BABA-AHMED

TASIRIN SA: Shi ne mafi kankantar shekaru a cikin ‘yan takarar 12. Mai ilmi ne sosai, kuma shi ne ke da mashahuriyar sabuwar jami’ar nan ta Baza University, da ke Abuja. Idan aka yi wani juyi aka ce sabbin jini za a zaba, to Baba-Ahmed ne zai ci kai-tasaye.

CIKAS: Matsalar Baba-Ahmed ita ce idan masu zabe suka rufe ido suka ce sai mai kumbar susa za su zaba, to tun daga tashin farko za a tsare masa fintankau.

SAURAN ’YAN TAKARA: ‘Motsi Ya Fi Labewa’

Za a iya yi wa sauran ‘yan takara irin su Attahiru Bafarawa, David Mark, Jonah Jang da Kabiru Turaki kudin-goro. Ana ganin cewa sun dai fito ne domin yin irin abin da Hausawa ke cewa ‘motsi ya fi labewa.’ Ko a yankin Arewa ta Tsakiya inda Mark da Jang suka fito, ba kowane wakilin da zai yi zabe ba ne zai zabe su.

Haka Bafarawa da Turaki da suka fito daga yanki daya, wato Arewa maso Yamma, bas u yi tasiri sosai ba. Don haka su hudun za a iya ce musu ‘kadaran kadahan.’

Share.

game da Author