Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta tunatar wa jam’iyyun siyasa cewa ranar 7 Ga Oktoba ce za a kammala duk wani zaben fidda-gwanin kowane mukami da za a yi takara a zaben 2019.
Haka kuma INEC ta za a wannan rana ce wa’adin ranar da za a sasanata kowane irin rashin jituwa da tashin-tashinar tankiyar zaben fidda-gwani da ta taso, tare da korafe-korafen ‘yan takara.
Wannan sanarwa ta fito ne a cikin wata katardar bayani da Kwamishinan Zabe na Kasa, kuma Shugaban Wayar da Kan Jama’a, Solomon Soyebi ya fitar a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce jam’iyyu 89 daga cikin 91 da suka nemi iznin fara yin zabukan fidda-gwani, na ci gaba da gudanar da zabukan kamar yadda Dokar Zabe ta 2010 ta ba su damar yi.
Ya ce dole jam’iyyu su kammala zabukan fidda-gwani da sasanta korafe-kofare ya zuwa ranar 7 Ga Oktoba, 2018, kamar yadda tun da farko jadawalin matakan zaben 2019 ya gindaya.
Daga nan sai kara nanata cewa ranar 18 Ga Oktoba ce ranar karshe da INEC za ta karbi fom din zababbun ‘yan takarar shugaban kasa na ‘yan majalisar tarayya.
Ranar 2 Ga Nuwamba kuma za ta rufe karbar fom din zababbun ‘yan takarar gwamna da na majalisar jihohi.
Soyebi ya kara nanata cewa INEC ba za ta karbi fom daga hannun kowane dan takara ba. Shugaban jam’iyya ne da sakataren sa za su kawo fom din kowane dan takarar da aka zaba domin ya wakilci jam’iyyar sa a matakin zaben da ya fito takara.
Discussion about this post