Bayan mutane 13 da aka kashe ranar talata a kauyen Jol jihar Filato, an sake far wa kauyen Ariri dake karamar hukumar Bassa inda aka kashe wasu mutane har 19.
Wani shugaban kungiyar ci gaban garin Irigwe, Sunday Abdu, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa an kawo wa mutanen garin hari ne cikin dare.
” Maharan sun shigo mana a cikin dare ne a daidai mutane suna bacci.”
Abdul ya ce tuni mutanen garin suka sanar wa ‘yan sanda abinda ya faru.
Sai dai kuma jami’an tsaro da aka tattauna da sun ce suna nan suan bin diddigin abin tukuna kafin su fitar da bayanai a kai.