Yara miliyan 13.2 ne basu zuwa makaranta a Najeriya – UBEC

0

Shugaban hukumar kula da ilimi (UBEC) Hammid Bobboyi ya bayyana cewa bisa ga binciken da asusun bada tallafi wa kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta gudanar a shekaran 2015 ya nuna cewa adadin yawan yaran da basu zuwa makaranta a Najeriya ya karu daga miliyan 10.5 zuwa 13.2.

Bobboyi ya fadi haka ne ranar Alhamis a taron karkato da hankulan sarakunan gargajiya game da wannan matsala da ke neman ya fi karfin kasar a Abuja.

Bobboyi ya ce hakan na da nasaba ne da aiyukkan Boko Haram da Najeriya ta yi fama da su a shekarun da suka gabata sannan da yawan haihuwa da ake samu.

” Idan aka kwatanta yawan yaran da basa zuwa makaranta saboda aiyukkan Boko Haram sannan da wadanda aka haifa za a ga yawan ya kai miliyan 13.2 a maimakon miliyan 10.5 din da muka sani a da.

Ya ce a dalilin aiyukkan Boko Haram gwamnati ta kasa kirkiro kudirorin da za su inganta fannin ilimi domin wadannan yara su sami ilimin Bokon da suke bukata.

Bobboyi ya ce a dalilin haka ne suke kokarin karkato da hankulan sarakunan gargajiya a sami makfita ga wannan matsala.

Bayan haka jami’in UNICEF Terry Durnnian ya bayyana cewa za su taimakawa wa Najeriya ne kawai amma shawo kan wannan matsala ya rage wa kasar ta nemi mafita da kan ta.

Sannan ya kara da ba kasar shawara kan ware wa fannin kiwon ilimi na kasar.

Share.

game da Author