Zaben ‘yan takarar APC da aka gudanar a Kano domin fidda gwanin sanatocin shiyyoyi uku, ya fitar da wadanda suka yi nasara, da suka hada da sanatoci biyu da ke a kai yanzu, Sanata Kabiru Gaya, Barau Jibrin da kuma sabon shigowa takara, tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.
Da ya ke bayyana sakamakon zaben Kano ta Kudu, jami’in zabe Balarabe Jakada, ya bayya cewa Gaya ya samu kuri’a miliyan 1,035,057, shi kuma Abdulrahman Kawu 309,209 sai Isa Zarewa mai kuri’u 15,543.
Shi kuwa jami’in zaben Kano ta Tsakiya mai suna Saleh Garba, ya bayyana cewa Shekarau ya samu kuri’a 973,435.
Laila Buhari ta zo ta biyu da kuri’u 3,004 sai kuma Sulaiman Halilu da ya zo na uku da kuri’u 1001.
Shiyyar Kano ta Arewa kuwa, Sanata Barau Jibrin ne ya sake samun damar tsayawa takara, ba tare da abokin hamayya ba, bayan janyewar ‘yan takara biyu, Abdullahi Tijjani da Mohammed Gwarzo.
Discussion about this post