Dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Aminu Tambuwal, ya bayyana cewa zai sake fasalin tarayyar kasar nan idan ya zama shugaban kasa a zaben 2019.
Tambuwal wanda shi ne gwamnan Sokoto, ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi ga taron ‘yan jam’iyyar PDP a Lagos, ranar Laraba.
Kamfanin Dillancin Najeriya ya ruwaito cewa ziyarar da ya kai wa jam’iyyar a Lagos na daga cikin rangadin neman goyon bayan da Tambuwal din ke yi a fadin kasar nan.
Ya ce a shirye ya ke karfafa tare da daukaka kima da martabar tattalin arzikin kasar nan yadda Najeriya za ta samu bunkasa , domin ya na da gogewar sanin makamar shugabanci.
Tambuwal ya ci gaba da cewa ya na da masaniya da gogewa gami da gogayyar duk wata logar shugabanci, shi ya sa ya fito takara, tare da fatan za a yi amanna da shi a kuma damka masa amanar Najeriya yadda zai kai ta gaci.
“Zan iya jagorancin Najeriya ta kai ta ga zama mashahuriyar kasa. Saboda na san shugabanci, na yi kakakin majalisar tarayya kuma na yi gwamna.
Ya kara da cewa Najeriya na fuskantar gagarimar matasalar tattalin arziki da kuma matsalar tsaro da ke bukatar shugaban da ya fi cancanta ya kawo mafita.
Daga nan sai Tambuwal ya ce idan har aka ba shi dama, to zai shawo kan wadannan matsalolin cikin kankanen lokaci.
Ya kuma nuna damuwar sa ganin yadda mashahuriyar jiha kamar Lagos, amma jam’iyyar PDP ba ta taba mulki a jihar ba.