2019: Jami’an SSS na barazanar yi wa sake zaben Buhari kafar-ungulu

0

Nada Yusuf Bichi da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi a matsayin sabon Darakta-Janar na SSS, ya haifar da guna-guni da tayar da kayar-baya a tsakanin manyana jami’an, har wasu na barazanar yi wa sake zaben Muhammadu Buhari kafar-ungulu.

Ba zaben kadai za su yi wa zagon-kasa ba, sun yi barazanar yi wa shirin yaki da Boko Haram tarnaki da dabaibayi.

Jami’an SSS da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa manyan jami’an ‘yan sandan leken asirin na hedikwata a Abuja da kuma wadanda ke fadin jihohi, sun rika harbin-iska tun bayan da Buhari ya sake kiran Yusuf, bayan da ya rigaya ya yi ritaya, ya canji Matthew Seiyefa a ranar 13 Ga Satumba, 2018.

An cire Seiyefa wata daya da ‘yan kwanaki bayan Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya nada shi bayan cire Lawan Daura.

Seiyefa yayi alkawarin yin aiki daban, ba irin wanda Lawan Daura ya rika yi ya na garkame mutane bagatatan ba.

Cikin makonni biyu bayan hawan sa, ya saki wasu da aka ‘tsare ba bisa doka ba’ kuma ya nada wa hukumar tsaro ta SSS kakakin yada labarai, mukamin da babu duk tsawon lokacin da Lawal Daura ya yi shugaban ta.

KATSALANDAN DIN ABBA KYARI

Kwanaki kadan kafin cire Seiyefa, PREMIUM TIMES ta gano cewa wasu ‘yan ba-ni-na-iya da ke fadar shugaban kasa, musamman Abba Kyari na neman ganin an cire shi.

Majiya a fadar shugaban kasa ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa Kyari bai ji dadin cire Lawal Daura da Osinbajo ya yi ba.

Ganin haka, sai Kyari ya nemi ya rika kanannade wasu ayyukan Seiyefa a hukumar SSS, ciki kuwa har da inda za a tura wancan da wancan da wasu ‘yan nade-nade. Kuma ya ba shi umarnin rika bin umarnin da fadar shugaban kasa za ta rika bashi daga lokacin.

Da farko Seiyefa ya nemi cirjewa ya nuna kin amincewa ya zama ‘boyi-boyin’ shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya na mai nanata cewa shi fa Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro ne kadai ogan sa, kuma shi zai rika kai wa rahoto, kamar yadda dokar aikin sa ta tanadar.

Amma daga baya sai Seiyefa ya kwantar da kai ya rika yin yadda Abba Kyari ke so ya rika yi.

Wasu manya da karabitin SSS da suka zanta da PREMIUM TIMES a lokacin da ya ke sa-toka-sa-katsi da Kyari, sun jaddada goyon bayan su ga Seiyefa tare da suna cewa ba za su taba yarda a zubar da kimar aikin SSS ba, ta hanyar cusa siyasa a cikin aikin.

Sannan kuma Seiyefa ya samu goyon bayan wasu daga cikin shugabannin Kudancin kasar nan, wadanda ba su ji dadin yadda aka cire dan kudu daga aikin shugabancin hukumar tsaron ta SSS ba.

Lokacin da Buhari ya cire Seiyefa, an rika guna-gunin cewa an cire shi ba wai don bai cancanta ba ko don bai iya aiki aiki ba. Amma dai saboda Buhari bai gamsu da a ce wani dan kudu ne zai shugabanci hukumar tsaro ba a lokacin da za a gudanar da zaben da shi Buhari ke son ganin ya yi nasara matukar gaske.

Bayan an cire Seiyefa, sai wasu shugabanni daga Kudancin da Tsakiyar kasar nan suka zargi Buhari da laifin rura wutar bangaranci da addinanci a kasar nan.

Sun ce Buhari ya yi watsi da wasu manyan jami’an SSS da dama ‘yan kudu, sai ya koma ya dauko wani tsohon jami’in da ya rigaya ya yi ritaya. Hakan a cewar su Buhari ya nuna bai yi imani da kasancewar Najeriya kasa daya dunkulalliya ba.

Edwin Clark da Ayo Adebanjo ne suka yi wa Buhari tatas, a cikin wata takardar bayan taro da suka fitar a lokacin.

Cikin Afrilu Buhari ya ayyana sake tsayawar sa takara. Hakan ya sa wasu manyan jam’iyyar APC irin su Atiku Abubakar ficewa daga jam’iyyar.

Wani bincike na musamman da PREMIUM TIMES ta gudanar ya nuna cewa Buhari na fuskantar barazanar yiwuwar sake zaben sa. A wannan karo, ba daga ‘yan adawa ba, sai daga jami’an tsaro na farin kaya.

A makon farko bayan an nada Bichi, wasu daraktocin SSS su hudu sun yi hira da PREMIUM TIMES daban-daban, inda kowanen su ya nuna rashin jin dadin abin da Buhari ya yi.

Wata karin tattaunawa da wasu manyan jami’ai takwas da kananan jami’ai biyar, sun tabbatar da rashin jin dadin su da wannan nadi da Buhari ya yi wa Bichi.

MASU TSORON YIN GIRMAN KWABO

Manyan jami’an SSS na guna-guni da fargabar cewa idan haka za a rika tafiya, ga su da girman su a cikin gwamnati, amma ba za a rika nada shugabannin SSS a cikin su ba, sai a rika zabowa cikin wadanda suka yi ritaya (Kamar yadda Buhari ya dauko Lawal Daura da Yusuf Bichi), to su haka za su kare a girman-kwabo kenan ba tare da yin shugabancin hukumar ba.

“Afakriya Gadzama, Ita Ekpeyong, Lawal Daura da Mathew Seiyefa duk sun yi shugabanci, kuma dama ‘yan zamani daya ne. Amma yanzu tsarar mu babu wanda ya kai zama shugabancin hukumar.”

Shi ma wani babban jami’i daga Arewa yace ba zai taba yafe wa Buhari da ya maido Yusuf Bichi bayan ya yi ritaya ba.

“Wannan mutumin fa ya yi ritaya tun cikin 2015, sai ya rika yin wata kwangila tsakanin sa da Lawan Daura tsawon shekaru biyu, zuwa 2017. To don me za a maido shi shekaru uku bayan ya yi ritaya kuma?”

“Mun yi imani da cewa shugaban kasa ya yi haka ne don ya kare kujerar mulkin sa, amma za mu tabbatar da cewa bai sake cin zabe ba.”

Wani darakta na SSS ma cewa ya yi, “ko dai mu yi wa ‘yan adawa aiki ko kuma mu kawo wa yakin Boko Haram cikas, amma sai mun fitar da shi daga ofis.”

Kokarin jin ta bakin hukumar SSS ya ci tura a lokacin da aka rubuta wannan labarin.

Share.

game da Author