ZABUKAN FIDDA GWANI: Gwamnonin APC na ganawar Sirri da Buhari a Aso Rock

0

Wasu daga cikin gwamnonin APC suna ganawar sirri da shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati dake Abuja.

Ko da yake ba sanar da makasudin wannan ganawa ba, alkaluma sun nuna cewa ganawar na da nasaba da rikice-rikicen da ake fama dasu a jam’iyyar musamman wadanda suka shafi zabukan fidda gwani da aka yi a jihohin kasar nan.

Gwamnonin da suke halartar ganawar sun hada da na Zamfara Abdulaziz Yari, Rochas Okorocha na jihar Imo, Rotimi Akeredolu na jihar Ondo da Abubakar Bello na jihar Neja, Ibikunle Amosun na jihar Ogun, Atiku Bagudu na jihar Kebbi, Abiola Ajimobi na jihar Oyo da Simon Lalong na jihar Filato.

Share.

game da Author