Kwamitin Zartaswa na Kasa, na jam’iyyar APC ya soke zaben fidda-gwanin ‘yan takarar gwamna na jihar Zamfara.
A cikin wata sanarwa da kakakin yada labarai na APC mai riko, Yekini Nabena ya saka wa hannu, a safiyar yau Alhamis, ba ta bada sanarwar ranar da za a sake zaben ba, amma ta yi alkawarin za a sake gudanar da zaben da gaggawa.
An sha daga zaben a baya saboda wasu dalilai, a jiya kuma rashin isar kwamitin gudanar da zaben daga Abuja kan lokaci ya sa aka dage zaben.
Da farko 1 Ga Oktoba aka shirya gudanar da zaben, amma hargitsi ya sa aka soke.
Kwamitin shirya zabe na jiha sun zargi gwamna Yari da yi wa zaben kafar-ungulu, abin da ya kaifar da rigima a wasu wurare.
A jihar dai sauran ‘yan takara bakwai sun nemi hada kai da nufin a kayar da wanda gwamna ya tsaida tun farko ya ce shi ne zai fito takara.
Wadanda hukuncin da gwamnan ya yanke bai masu dadi ba, ciki har da mataimakin sa Ibrahim Wakkala, sun tuma tsalle sun yanki fom, kuma sun ce sai an yi zaben fidda-gwani na tsarin kato-bayan-kato.