Buhari ya yi magana da mahaifiyar Leah Sharibu

0

Shugaba Muhammadu Buhari, ya kira mahaifiyar Leah Sharibu sun yi magana ta waya.

Buhari ya shaida wa Rebecca cewa gwamnatin sa na bakin kokarin ganin an karbo ta daga hannun ‘yan Boko Haram, wadanda ke rike da ita, tun bayan da suka sace daliban sakandaren Dapchi.

Sun rike Leah ne tun bayan da aka sace ta tare da da dalibai 109, saboda ta ki musulunta.

Kakakin Yada Labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka yau a cikin Fadar Shugaban Kasa.

Tun bayan da aka rike Leah dai gwamnatin Buhari ke shan matsi-lambar a kokarta karbo ta.

Sanarwar da Garba Shehu ya bayar yau, ta tabbatar da cewa Buhari ya taya Rebecca, mahaifiyar Leah jimami, tare da tabbatar musu da cewa gwamnatin sa za ta tabbatar da cewa ta karbo Leah kuma an tsare lafiyar ta.

Buhari ya shaida wa Rebecca cewa ‘yar su Leah shi ma ‘yar sa ce, a matsayin sa na shugaban kasar nan.

Share.

game da Author