JIHAR YOBE: Ba ayi zaben gaskiya a zaben fidda dan takarar gwamna na APC ba – Umar Ali

0

Dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar APC Umar Ali ya yi Allah wadai da sakamakon zaben fidda gwanin da akayi a jihar Yobe.

Bisa ga sakamakon zaben da aka bayyana sakataren jam’iyyar APC na kasa Mai Mala Buni ne ya lashe zaben da kuri’u 2,79, Sidi Karasuwa ya sami kuri’u 23, umar Ali kuri’u 8 sannan Aji Kolo, 0.

Ya kuma ce takardun zaben da aka yi amfani da su a wannan rana ba daidai suke ba da wadanda aka yi amfani da su a saurarn jihohin kasar nan kamar su Barno da Katsina .

” Bisa binciken da muka yi wasu daga cikin takardun zaben basu dauke da tambarin jam’iyyar APC.

A karshe Ali ya yi kira ga uwar jam’iyyar da ta gaggauta soke wannan zabe da aka yi gaba daya.

Share.

game da Author