2019: Ba mu amince da zabin Shehu Sani dan takara Tilo a Kaduna ba

0

Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kaduna ta tsakiya, Aminu Jibo ya bayyana cewa reshen jam’iyyar a Kaduna ta tsakiya ba za ta amince da zabin Sanata Shehu Sani a matsayin dan takara tilo ba kamar yadda uwar jam’iyyar ta yi.

Jibo ya ce abin da jam’iyyar ta yi ba daidai bane sannan su a jihar Kaduna ba za su amince da haka ba.

Tun bayan fitar da jerin sunayen ‘yan takara da jam’iyyar APC ta yi ranar Talata aka fada cikin rudani a jihar Kaduna domin kuwa wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar suka dunguma zuwa ofishin jam’iyyar na jiha don nuna rashin amincewar su ga yakice wasu ‘ya’yan jam’iyyar da aka yi bayan kuwa sun sayi fom din tsayawa takara.

” Wannan abu bai yi mana dadi ba kuma ba za mu amince da haka ba. Mutane kamar su Mal Uba Sani da suka bauta wa jam’iyyar a jiha sannan suka sadaukar da komai na su domin ganin jam’iyyar ta tsayu da kafafuwan ta biyu a jihar amma kuma sai kawai a yi watsi dasu bayan sun sayi fom din kuma sun fito takara.

” Jam’iyyar bata yi wa wadannan ‘yan takara adalci ba kuma muna kira ga jam’iyyar da ta gaggauta yin gyara ko kuma mu dauki mataki kai tsaye game da haka.

” Ba zai yiwu ace wai wadanda suka nemi gurgunta tafiyar jam’iyyar a jiha ne za a nada da karfin tsiya sannan kuma ace an yi wa jam’iyya adalci. Ba za mu amince da haka ba.” Inji jibo

Har yanzu dai jam’iyyar APC bata ce komai ba akai duk da zanga-zanga da wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi Kaduna.

Share.

game da Author