Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), Samson Ayokunle, ya bayyana cewa kungiyar su ta kiristoci ta kammala shirin yi wa kiristoci 300 taron bita da kuma bayar da horo, wanda za su yi domin aikin sa-ido su ga yadda za a gudanar da zaben 2019 a fadin kasar nan.
Ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron Kiristoci da aka gudanar a Legas jiya Litinin.
Samson yace za a tattaro masu sa-idon ne daga kowace sashe na shiyyoyin kasar nan, inda horaswar da za a yi musu za ta ci kudi har naira miliyan 12.
“ Za a bada horo ga mutane hamsin daga kowace shiyya, su kuma su je su gayar da horo saura.
“Shirin da muke yi shi ne kowace rumfar zabe, za mu tura masu sa-ido uku, domin tuni har mun aika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) takardar neman amincewar ta.
“Ya ce ita ma INEC sai ta kara tashi tsaye, idan aka yi la’akari da yadda zaben jihar Osun ya gudana, inda aka samu rikice-rikice, sayen kuri’u da kuma cin zarafin jama’a.
Ya kara da cewa kungiyar su a shirye ta ke ta yi aiki kafada da kafada da kungiyar Musulmi, domin shata abubuwan da ake hasashen dan takara zai iya kasancewa ya na da su, da kuma abin da zai kara kawo hadin kai wajen gudanar da sahihin zabe.
Discussion about this post